Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin zambar N110bn

yahaya bello sad new

Gwamnatin tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume 16 a kan Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi.

Laifukan da aka gabatar a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, sun ce ana tuhumar sa da laifin karya amana da suka kai N110,446,470,089, wanda ya saba wa sashe na 96 da 311 na kundin Penal Code Law Cap.

Laifin yana da hukunci a karkashin sashe na 312 na wannan doka. Bello, wanda a baya yana fuskantar tuhume-tuhume 19 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da shi tare da wasu jami’an gwamnatin Jihar Kogi biyu, Abdulsalami Hudu da Umar Oricha.

Takardar tuhumar ta nuna cewa mutanen ukun sun karkatar da wasu kudade daga baitul malin jihar Kogi domin su mallaki kadarori a Abuja da Dubai.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya zargi wadanda ake tuhumar da hada baki wajen aikata wani laifi a shekarar 2016 a Abuja da ya hada da Naira biliyan 110.4.

Sauran tuhume-tuhumen sun hada da zargin cewa sun yi amfani da Naira miliyan 950 a shekarar 2023 wajen mallakar wani katafaren gida mai lamba 35 a titin Danube, Maitama, Abuja, da kuma Naira miliyan 100 a shekarar 2021 wajen siyan wata kadara a gundumar Gwarimpa I, Abuja.

Karin tuhume-tuhumen sun ce an yi amfani da Naira miliyan 920 a shekarar 2020 kan wata kadara a Asokoro, Abuja, yayin da kuma aka yi amfani da Naira miliyan 170 wajen mallakar dukiya a Wuse Zone 4 a shekarar 2022.

An yi zargin an siya kadarori a gundumar Guzape da Lome Street a Abuja kan Naira miliyan 100 kowanne a shekarar 2018 da 2020, bi da bi.

Sauran abubuwan da aka samu a Wuse 2, gundumar Maitama, da Dubai sun kai na daruruwan miliyoyi.

Wata shari’a ta kuma ce wadanda ake tuhumar sun kashe sama da Naira miliyan 310 a shekarar 2017 don gyara wata kadara a Wuse Zone 4.

Bugu da kari, tuhume-tuhume biyu na zargin sun tura sama da dala miliyan 1 zuwa asusun bankin TD a Amurka a shekarar 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here