Gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin alawus na masu hidimtawa kasa daga N33,000 zuwa N77,000, wanda hakan zai fara aiki daga watan Yuli 2024.
Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) ta sanar da karin alawus dinne a yammacin ranar Laraba a shafinta na Facebook.