Bankin Afirka ya tallafawa Najeriya da Dala Miliyan 540

gwamnati, 'yan kasuwa, jiha, sokoto, kayan abinci, najeriya, garuruwa
Gwamnatin Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya ta sanar da hana fitar da kayan abinci domin shawo kan tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin da ake fuskanta...

Bankin raya kasashen Afirka, ya fara raba tallafin kudi har Dalar Amurka Miliyan 540 ga wasu jihohin Najeriya 8, a wani yunkuri na samar da isasshen abinci ga al’umma tare da kuma sarrafa shi, yayin da ‘yan kasar ke kokawa kan tsadar rayuwa.

Sanarwar ta fito ne ta bakin mai bawa shugaban bankin shawara na musamman Farfesa Banji Olareyen Oyeyenka wanda ya bayyana cewa.

“Mun tanadi Dala Miliyan 540 da za mu rabawa Jihohi 8 domin rabawa manoma, don bunkasar jihohin daya bayan baya” Inji Olareyen.

Karanta wannan: Super Eagle: ‘Yan Afirka ta Kudu na barazanar kaiwa ‘yan Najeriya hari

Ya kara da cewa, “Mun kakkafa wuraren gudanar da ayyukan da suka hada da tattara bayanai, yanzu mun kai matakin rarraba tallafin ga jihohi 7 ciki har da babban birnin tarayyar Abuja.”

A halin da ake ciki kasar nan da ke yammacin Afirka farashin kudin masara da buhun shinkafa ya ninka mafi karancin albashi.

Haka zalika, kuma hauhawar farashin kaya ya jefa kananan ‘yan kasuwa cikin zulumi sakamakon karyewar darajar kudin kasar, inda Dalar Amurka ke ci gaba da tashin gwauron zabi.

Karanta wannan: “Gazawa ce APC ta fito tana zargin ‘ƴan adawa” – Jam’iyyun Adawa

‘Yan Najeriya dai na ganin gazawar gwamnatin kasar nan wajen dogaro da man fetur alhalin kasar na da arzikin ma’adanai da na noma.

Masana dai na ganin cewa rashin fitar da kayayyaki zuwa kasuwar duniya, da kuma dogaro da kayan kasashen waje ne, abin da ya jefa kasar nan cikin halin tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here