Za a Toshe Sadarwa a Jihar Kaduna- El-Rufai 

el rufai Speaking 1
el rufai Speaking 1

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci mazauna jihar da su shirya saboda za a rufe sadarwa a jihar.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a hirarsa da wasu gidajen rediyon jihar a ranar Talata, inda ya ce jami’an tsaro a shirye suke su kaddamar da farmaki kan ‘yan fashi da ke fakewa a wasu sassan jihar.

Gwamnan ya ce rufewar ba za ta shafi jihar baki daya ba, ya kara da cewa kananan hukumomin da ke makwabtaka da Zamfara da Katsina inda ake ci gaba da kai farmaki na sojoji ne abin zai shafa.

“Sojoji da sauran hukumomin tsaro sun shawarce mu da mu rufe ayyukan sadarwa a wasu kananan hukumomi amma muna jiran hukumomin tsaro su gaya mana takamaiman wurare da kuma lokacin,” in ji El-Rufai.

“Amma ina son mutanen jihar Kaduna su sani cewa idan sun ba mu go-goben gobe [Laraba], za mu rufe gobe.”

Gwamnan ya ce saboda rufe ayyukan sadarwa a Zamfara da Katsina, wasu ‘yan bindiga sun tsallaka zuwa kananan hukumomin makwabta a Kaduna don yin kiran waya da neman fansa.

Gwamnan yace “Ba zan ambaci kananan hukumomin da abin zai shafa ba amma kananan hukumomin da ‘yan bindiga ke azabtar da su kullum sun san kansu,”.

“Da zaran mun samu bayanai daga jami’an tsaro, to yakamata jama’ar jihar Kaduna su sani cewa za mu rufe hanyoyin sadarwa don baiwa jami’an tsaro iyakar hadin kai don gudanar da ayyuka a wadannan yankuna.

El-Rufa’i ya kuma ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti wanda zai zagaya yankunan bayan gari don sa ido kan bin wasu matakan tsaro da jihar ta dauka don tabbatar da an rufe gidajen mai da kasuwanni don ci gaba da tokare ‘yan fashi a dajin.

Yayin da yake ba da shawara ga mazauna yankin kan bukatar ganowa da bayar da rahoton masu ba da labari ko masu hannu da shuni, El-Rufai ya ce: “Duk wanda ya zo siyo burodi 20 zuwa 100, ya sayar masa amma kuma ya san ar da jami’an tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here