Bikin Ýancin Kai: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Juma’a, 1 ga Oktoba, a Matsayin Ranar Hutu

Rauf Aregbesola. 2
Rauf Aregbesola. 2

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 1 ga Oktoba, a matsayin ranar hutu don murnar cikar kasar shekaru 61 da samun ‘yancin kan kasar.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da Dr Shuaib Belgore, babban sakataren ma’aikatar ya fitar a madadinsa, ministan ya taya dukkan ‘yan Najeriya murnar bikin wannan shekarar tare da ba da tabbacin jajircewar gwamnati na magancewa da kawar da duk wasu kalubale.

Ministan ya ce, duk da yin bikin cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai ya zama dole, amincin dan kasa shine babban abin da shugaban ya damu da shi, musamman saboda cutar COVID-19 samfurin Delta har yanzu tana nan.

“Don haka, za a gudanar da bikin wannan shekarar ba tare da nuna wani shagulgula da yawa ba,” in ji shi.

Yayin da yake yiwa ‘yan Najeriya murnar samun’ yancin kai, ya tunatar da su cewa jagororin da suka kafa mu, ba tare da banbancin addini ko kabila da yare ba, sun hadu don samarwa Najeriya’yancin kai.

Don haka, ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su hada hannu da gwamnati mai ci a kokarinta na tabbatar da ingantacciyar Najeriya ga dukkan’ yan kasa, a gida da waje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here