
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da cewa wani mai suna Olumide Openaike ma’aikacin bankin Microfinance Kemta Oloko, ya ba da rahoton bacewarsa kuma aka same shi a Mokwa da ke jihar Neja ya yi karyar garkuwa kan bashin Naira Miliyan 1.7m.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola ta tabbatarwa da manema labarai hakan a ranar Talata.
Matar ma’aikacin bankin, Temitope, ta shaida wa manema labarai yadda mijinta, Olumide ya bace a ranar 17 ga watan Janairu a kan hanyarsa ta zuwa aiki.
Karanta wannan: Hukumar NDLEA ta kama mutane 198 da ake zargi
Temitope ta shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, “Na yi farin cikin gaya muku cewa an samu mijina a wani wuri da ake kira Mokwa a Jihar Neja. Ya kira ni ranar Talata da yamma.
“Ya samu waya daga wurin daya daga cikin mazauna wurin saboda ya ce wadanda suka sace shi sun karbi wayarsa. Sai muka ce masa ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda da ke wurin, dan sandan da ke bakin aiki da ya zanta da mu ya ce yana Mokwa.
“Sai aka shirya kudin jigilar kaya aka aika masa, ya isa Ibadan jiya Laraba kuma ‘yan uwansa suna Ibadan. Yau zai dawo Abeokuta”.
Sai dai rundunar ‘yan sandan ta bayyana rahoton sace ma’aikacin bankin a matsayin na bogi ne.
Karanta wannan: An Dakatar Da Yar Nijeriya a Masalisar Burtaniya Kan Goyon Bayan Gaza
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Odutola ta ce, “Eh, ‘yan sanda sun gano cewa ma’aikacin bankin, Olumide Openaike ya yi karyar garkuwar ne kan bashin Naira Miliyan 1.7 alhalin kuma kudin na bankin da yake aiki ne.
“Abin da ya faru shi ne wani abokin ciniki yana tura kudin zuwa banki amma Openaike yana karkatar da su zuwa ga amfanin kansa, daga nan sai ya shiga damuwa kuma ya yanke shawarar yin karyar a sace shi.”











































