FCT: Duk mai son takardar shaidar Mallakar Fili a Abuja sai yana da NIN da BVN-Wike

Nyesom Wike FCT Minister
Nyesom Wike FCT Minister

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce samun takardar mallakar Fili ko Gida a Abuja a yanzu ba zai yiwu ba sai mutum yana da Lambar Shaidar zama dan Kasa wato NIN da kuma Lambar BVN.

Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Wike ya kuma ce wadanda tuntuni suka mallaki filaye a babban birnin tarayyar dole ne su sami takardar shedar wadannan sabbin tsare-tsare.

A cewar ministan, ya bullo da wadannan ingantattun matakai ne domin tabbatar da tsaro, saboda haka daga yanzu ga daidaikun mutane duk wanda ke son mallakar Fili sai ya bada lambar NIN, yayin da Kamfanoni kuma za’a bukaci su bayar da lambar BVN.

Wike ya kuma bayyana fa’idodin da za’a iya samu a sanadiyyar wannan yunkuri musamman wajen gano mamallaka kadarori domin biyan haraji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here