Qatar ta ayyana jami’an soja da na tsaro na ofishin jakadancin Iran da ke Doha, tare da ma’aikatansu, a matsayin wadanda ba za a yi maraba da su ba.
Ma’aikatar harkokin wajen Qatar, a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Laraba, ta bukaci jami’an da su bar kasar cikin sa’o’i 24, kamar yadda Al Jazeera ta rawaito.
Qatar ta bayyana cewa matakin da ta dauka ya biyo bayan hare-hare da Iran ke kai mata akai-akai.
Rahotanni sun nuna cewa sabon harin da Iran ta kai ya kai hari kan mafi girman filin iskar gas na Qatar.
Kamfanin QatarEnergy ya bayyana cewa an harba makamai masu linzami zuwa kamfanin Ras Laffan lamarin da ya haddasa gobara mai yawa da kuma barna mai girma.
Rahotanni a n ce an riga an kwashe mutane daga wurin kafin harin, bayan Iran ta yi barazanar kai hari kan wurin da wasu wurare hudu a yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan filayen iskar gas nata.
Iran na kai hare-hare kan muradun Amurka a yankin Gulf tun bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai mata ba tare da tayar da wata fitina ba.













































