Kaduna: Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi Shugaba Buhari

IMG 20250919 WA0008 750x375 1

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara ga iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Kaduna, bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Tinubu ya isa gidan marigayin inda ya samu tarba daga gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, da sauran danginsa.

A lokacin ziyarar, Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Hajiya A’isha Buhari, tare da sauran ’yan uwa.

Ya sake yin ta’aziyya, inda ya shaida mata cewa zai ci gaba da ɗaukaka gadon shugabanci da Buhari ya bari.

Ya ce dangin ba su kaɗai ba ne cikin jimami, domin al’ummar Najeriya na tare da su.

Tinubu ya bayyana cewa Buhari ya bar wa Najeriya ɗabi’u na gaskiya, amana, ƙwazo, da kishin ƙasa, waɗanda gwamnati za ta ci gaba da tafiya a kansu.

Ya roƙi Allah ya taimaki ƙasar, ya ƙara haɗa kan ’yan Najeriya don ci gaba da tafiya zuwa ƙasar da ake mafarki.

Da take mayar da martani cikin muryar tausayi, A’isha Buhari ta gode wa shugaban ƙasa da iyalinsa bisa tallafi da goyon baya da suka nuna wa danginta a lokacin makoki.

Ta bayyana cewa wannan ziyara ta zama babban ta’aziyya ga iyalanta.

Hajiya A’isha ta kuma jaddada cewa marigayin mijinta ya tsaya kan gaskiya, rikon amana, adalci, da sahihancin shugabanci, inda ta roƙi ’yan Najeriya da su yi koyi da irin halayensa.

Ta kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar, tare da roƙon Allah ya taimaki Tinubu wajen ɗorewa a kan gadon shugabancin Buhari.

Shugaban ƙasa ya samu rakiya daga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.

Haka kuma, gwamnonin Jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq; Yobe, Mai Mala Buni; Borno, Babagana Zulum; da Sakkwato, Ahmed Aliyu, sun kasance cikin tawagarsa.

Haka nan, ministoci da suka haɗa da Wale Edun na kuɗi, Atiku Bagudu na kasafi da tsare-tsare, Bello Matawalle na ma’aikatar tsaron cikin gida, da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, duk sun halarci wannan ziyara.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here