Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kwato tsabar kudi Naira miliyan 175,706,500, dala $220,965, mota G-Wagon da sauran kayayyaki daga hannun wani dan kwangilar soja a Abuja.
A cewar hukumar ta ICPC an kama kayan ne a wani samame da jami’an hukumar suka kai kan wani gini a Abuja.
Azuka Ogugua, kakakin hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ogugua ya ce bisa ga bayanan sirri, hukumar ta kai samame a wani gida da ke Wuse 2, Abuja, inda aka gano kayayyakin masu tsada.













































