Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi watsi da matakin da gwamnatn tarayya ta ɗauka na dakatar da albashin mambobin gamayyar ma’aikatan lafiya JOHESU bisa tsarin babu aiki babu albashi.
Ƙungiyar ta bayyana cewa umarnin da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na dakatar da biyan albashi ta hanyar tsarin IPPIS ya saɓa ka’idojin hulɗar ma’aikata da gwamnati tare da tayar da hankali a tsakanin ma’aikatan lafiya.
TUC ta ɗauki matakin a matsayin tsokana da cin zarafin ma’aikatan lafiya, tana mai cewa ba za a iya ci gaba da tattaunawa da ma’aikata ba alhali ana hukunta su a lokaci guda da matakan da ke cutar da rayuwarsu.
Ƙungiyar ta nuna cewa dakatar da albashin ma’aikatan lafiya da ke ceton rayuka a kullum abu ne na rashin tausayi kuma ba kishin ƙasa ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashi da tashin farashin man fetur.
Karin labari: Duk da manufar “babu aiki babu albashi”: JOHESU ta dage kan ci gaba da yajin aiki
TUC ta bayyana cewa ma’aikatan lafiya sun daɗe suna riƙe tsarin kiwon lafiya duk da mummunan yanayin aiki, don haka bai dace a hukunta su kan matsalolin da suka shafi tsarin gwamnati ba, tana mai cewa amfani da IPPIS wajen hana albashi cin zarafin ikon gwamnati ne da ƙungiyoyin kwadago ba za su amince da shi ba.
Ƙungiyar ta buƙaci a janye takardar umarnin nan take tare da dawo da dukkan albashin da abin ya shafa ba tare da sharadi ba, sannan a koma teburin tattaunawa cikin kwanaki Bakwai domin kauce wa rikicin masana’antu a ƙasa.
TUC ta bayyana cewa dukkan rassanta, majalisun jihohi da ta babban birnin tarayya an saka su cikin shiri, tare da nuna cewa duk wani tangarda ga ayyukan jama’a alhakin ma’aikatar lafiya ta tarayya ne idan ta zaɓi rikici maimakon tattaunawa.
NAN













































