Kotun koli a zamanta na yau Talata ta tabbatar da Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwanan jihar Osun.
Mai shara’a Emmanuel Agim, ya yin da yake karanta hukunci a yau Talata, ya tabbatar da nasarar Ademola Adeleke.
Idon za’a iya tunawa a baya Oyetola shida jama’iyyar sa sun shigar da kara mai lamaba ta SC/CV/510/2023, suna rokon kotun data yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara dake zamanta abuja ta yanke akan Nasarar Ademola Adeleke, sanan ta ayyana Oyetola a matsayin wanda yaci zabe ba Adeleke ba.