Hukumomi a Senegal sun toshe hanyoyin shiga shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Facebook da WhatsApp sakamakon kazamin rikicin da ya biyo bayan hukuncin daurin shekara biyu da kotu ta yanke wa jagoran ‘yan hamayya na kasar.
Daman gwamnatin ta ce za ta dau duk wani mataki da ya dace domin kare rayuwar al’umma da dukiyoyi bayan mutuwar mutane sakamakon rikicin.
Read also: Masana’antar Dangote ta ƙawata bikin baje kolin kayayyaki a birnin Lagos
Akalla mutum tara ne suka mutu a rikici tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga, bayan yanke wa Ousmane Sanko hukuncin a jiya Alhamis.
Ministan cikin gida, Antoine Diome a wani taron ‘yan jarida a cikin dare, ya ce an toshe kafofin ne, yana mai nuna takaicin abubuwan da suka faru.
Read also: Babbar jojin Najeriya ta rantsar da sababbin lauyoyi 57 da suka samu matsayin SAN
Rikicin ya fi baci a yankin Ziguinchor – (Zi-gan-shiyo)- da ke kudancin kasar, inda Mista Sonko ke rike da mukamin magajin gari.
Hukukuncin kotun da aka yanke a bayan idonsa na iya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen shekara mai zuwa.
Read also: Sojojin Rasha sun fara kai farmaki a Ukraine
An same shi da laifin nuna rashin ɗa’a, amma an wanke shi daga zargin aikata fyaɗe.













































