Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu tabbacin goyon bayan siyasa daga shugabannin al’ummar Igbo da ke jihar Kano, domin marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027.
An bayar da wannan tabbaci ne yayin wani babban taro tsakanin gwamnan da wakilan al’ummar Igbo a gidan gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Igwe Boniface Igweke, Eze Dioramma IV, Sarkin Igbo na Kano.
Read also: Hotuna: Yadda mataimakin gwamnan Kano kan harkokin daukar hotuna ya yi rabon tallafin kayan abinci
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce tawagar ta kunshi manyan shugabannin gargajiya, siyasa da na al’umma, ciki har da Hon. Chukuma Innocent Ogbu, PhD, mai ba gwamnan Kano shawara kan harkokin al’ummar Igbo, Hon. Chief Donatus Nwago, tsohon shugaban kungiyar Igbo Community Association a Kano da Chief Raphael Ngbidi, sabon shugaban kungiyar.
Da suke magana a madadin al’ummar, shugabannin sun bayyana shirinsu na hada kai tare da yin aiki tare, tabbatar wa gwamnan cewa an shawo kan rarrabuwar kawunan da ta kasance tsakanin mambobinsu a lokacin zaben 2023.
Sun sake jaddada kudirinsu na zaman lafiya da jituwa, tare da yaba kokarin gwamnatin jihar wajen samar da tsaro da yanayin da ya dace ga mazauna jihar da masu gudanar da kasuwanci.
Sarkin Igbo na Kano ya bukaci gwamnan da ya ci gaba da ayyukan raya kasa a Sabon Gari, musamman aikin New Road, Zungeru Road da Sarkin Yaki . Ya kuma bukaci tallafin gwamnati wajen kammala aikin Igbo House.
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya bayyana al’ummar Igbo a matsayin wani muhimmin bangare na Kano, tare da amincewa da irin gudunmawar da suka dade suna bayarwa wajen kasuwanci, zuba jari da bunkasar tattalin arzikin jihar.
Read also: Zaben 2023: Farfesoshi sun marawa Osinbajo baya
Ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na da hakki a tsarin mulki na zama da gudanar da kasuwanci a duk inda yake a kasar, yana mai cewa kabila ko addini bai kamata su zama abin da zasu kawo cikas ga hadin kai da zaman lafiya ba.
Dangane da ayyukan more rayuwa, gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan takwas domin fadada Igbo Road da Hausa Road zuwa hanyoyi masu layuka biyu, tare da sanya fitilun titi.
Ya kuma bayyana cewa an sake bayar da aikin New Road ga wani sabon dan kwangila bayan soke kwangilar tsohon, inda aka kara ware Naira biliyan uku domin kammala aikin kafin watan Janairu.
Gwamnan ya kara da cewa aikin fadada Zungeru Road da Sarkin Yaki Road, tare da sanya fitilun titi, ya kai kusan kashi 70 cikin 100 na kammalawa.
Ya yaba wa al’ummar Igbo bisa hadin kan da suke bai wa gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa kudaden shiga da suke bayarwa sun karu da kusan kashi 70 cikin 100 sakamakon ingantaccen bin tsarin biyan haraji.
Read also: DA DUMI-DUMI: Kotun daukaka kara zata sanar da ranar yanke hukunci kan rikicin APC a Kano
Gwamna Yusuf ya kuma yi kira da a marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, yana mai nuni da fahimtar da ake da ita kan karba-karban mulki tsakanin Arewa da Kudu da kuma bukatar ci gaba da shugabanci a kasa.













































