Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama wata mata mai shekaru 27 mai suna Hadiza Ibrahim bisa zargin satar kaya daga wani shago mai suna Green House da ke cikin Katsina, inda aka kiyasta kudin kayayyakin da aka sace sun kai Naira Miliyan 10.1.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, DSP Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar juma’a, inda ya ce babban jami’in tsaro na shagon ne ya kai rahoton kama matar a ranar 4 ga watan maris, yana bayyana ta a matsayin wadda ta saba aikata satar kaya a cikin birnin.
Ya kara da cewa an gano kayayyakin da aka sace sun kai kimanin Naira Miliyan 10,102,000, kuma an gano matar ne ta hanyar na’urar daukar hoto ta sirri inda aka hango ta tana satar kayayyaki daban-daban daga shagon.
Bayan nazarin bidiyon, jami’an tsaro sun sanya mata ido har zuwa lokacin da aka kama ta a wurin, sannan aka gudanar da bincike a gidanta inda aka kwato kayayyaki masu darajar wannan adadi.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai takalma guda 274, mayafai guda 37, kayan wasanni guda 67 da kuma kayan yara guda 54, sai hula guda 123 da safa guda 315 da kuma atamfofi guda 45.
Sauran kayayyakin sun hada da jakunkuna guda tara, kwali uku na taliya, turare guda 24 da kuma kwali biyar na sabulu, tare da jakar kayan ado da kuma buhun kayan dandano na girki.
Ya bayyana cewa an riga an tantance kayayyakin da aka kwato daga hannun matar, yayin da ake ci gaba da gano sauran wadanda abin ya shafa, sannan bincike ya nuna cewa matar tana da tarihin aikata irin wannan laifi kuma ta amsa laifin, inda aka gurfanar da ita a gaban kotu domin fuskantar hukunci, tare da gargadin masu shaguna da su kara tsaurara matakan tsaro domin kare harkokinsu daga ayyukan laifi.












































