Dalilin yin murabus ɗi na – Mataimakin gwamnan Kano

Comrade Aminu Gwarzo 750x430

Mataimakin gwamnan jihar kano, kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana dalilan da suka sa ya yi murabus daga mukaminsa.

Gwarzo ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya samo asali ne daga nauyin da ke kansa da kuma kishin kasa, ba wai amincewa da wani laifi ba.

A cikin wasikar murabus dinsa da ya aike wa gwamnan jihar kano, Abba Kabir Yusuf, kuma aka bai wa manema labarai a ranar juma’a, Gwarzo ya bayyana cewa ya sauka daga mukaminsa ne da kansa domin bai wa gwamnati da jihar damar ci gaba ba tare da wata tangarda ba.

Ya ce, “Ni Aminu Abdussalam Gwarzo, mataimakin gwamnan jihar kano, na mika murabus dinsa daga mukami daga ranar 27 ga watan maris 2026, bisa tanadin sashe na 306 kashi na biyu na kundin tsarin mulkin tarayyar nigeria na shekarar 1999 wanda aka yi wa gyara”.

Ya kara da cewa ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da nazari mai zurfi, tare da la’akari da halin da ake ciki da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma moriyar al’ummar jihar kano.

Gwarzo ya bayyana cewa bisa la’akari da halin da ake ciki, ya dauki wannan mataki ne cikin kishin kasa, domin bai wa gwamnati da jihar damar ci gaba ba tare da wata matsala ko tangarda ba.

Ya kuma jaddada cewa murabus din da ya yi na son rai ne kuma cikin kyakkyawar niyya, yana mai cewa bai kamata a dauki hakan a matsayin amincewa da wani laifi ba, illa dai wani mataki ne da ya dauka domin kare mutuncin hukumomi, darajar dimokuradiyya da kuma hidimar jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here