Wani malamin kwalejin fasaha ta jihar kogi ya rasu a cikin aji yayin da yake koyarwa

The late Kogi Poly Lecturer Mr Anslem Ojodomo 715x430

Wani malami a sashen nazarin gudanar da harkokin gwamnati na kwalejin fasaha ta jihar kogi, mai suna Anslem Ojodomo, ya rasu a cikin aji yayin da yake koyar da dalibai.

Shugaban makarantar, farfesa Salihu Avidime, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da mista John Onimisi, mukaddashin mai kula da hulda da jama’a na makarantar ya fitar a ranar juma’a.

Wannan lamari mai tayar da hankali ya zo ne kusan wata guda bayan rasuwar wani malami a makarantar, dakta Barnabas Akuba, wanda ya rasu jim kadan bayan kammala karatunsa na digiri na uku.

Rasuwar Ojodomo ta janyo damuwa da fargaba a tsakanin ma’aikata da dalibai, inda da dama ke tambayar yadda mutuwar ta faru ba zato ba tsammani.

Shugaban makarantar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da daukacin al’ummar makarantar, inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban abin girgiza zuciya a gare shi da kuma makarantar baki daya.

Avidime ya tuna cewa ya hadu da marigayin sa’o’i kadan kafin rasuwarsa, inda suka gaisa tare da musabaha.

Ya yabawa marigayin a matsayin ma’aikaci mai kwazo, mai tawali’u da sadaukar da kai, wanda ya bambanta kansa tun a matsayin dalibi har zuwa lokacin da ya zama malami.

Daliban da suka shaida lamarin sun bayyana cewa malamin ya fadi ne yayin da yake koyar da su, inda aka garzaya da shi wani asibiti kusa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Sun kara da cewa al’ummar makarantar sun shiga cikin yanayi na rashin tabbas, musamman ganin cewa an rasa malamai biyu cikin kankanin lokaci.

Anslem Victory Ojodomo malami ne mai digiri na biyu daga jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Anyigba, inda kwanan nan ya kare kudirin bincikensa na digiri na uku.

Ya fara aiki a kwalejin fasaha ta jihar kogi a shekarar 2021, kuma ya yi aiki a kwamitoci da dama.

Al’ummar makarantar sun jajanta wa iyalansa da mutanen yankin Igalamela/Odolu, tare da yi masa addu’ar samun rahama da gafara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here