Hotuna: Yadda mataimakin gwamnan Kano kan harkokin daukar hotuna ya yi rabon tallafin kayan abinci

IMG 20230420 WA0025
IMG 20230420 WA0025

Mataimakin gwamnan jihar Kano, a fanin daukar hotuna, Malam Aminu Dahiru Ahmad, ya raba tallafin kayan abinci ga shuwagabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale da kuma wasu daga cikin matasan da suke bawa jam’iyya gudummawa a karamar hukumar.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da Aliyu haruna Sabangida, Sarkin yakin Malam Aminu, ya fitar ranar Laraba a jihar Kano.


Sanarwar ta ce kayan tallafin sun hada da shinkafa, taliya da kuma kudin cefane.
Yayin rabon kayan tallafin wanda ya gudana a karamar hukumar Gwale, shuwagabannin jam’iyyar sun yabawa Malam Aminu bisa yadda yake bada gudummawa garesu da Yan jam’iyya da Kuma daidaikun mutane.

Sannan kuma sun yi godiya tare da fatan alkhairi ga mataimakin, da kuma adduar Allah tallafa Masa akan duk abinda yasa a gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here