Diezani ta bayyana a gaban kotu a Landan kan shari’ar cin hanci Fam Dubu Ɗari

Diezani Alison Madueke 750x430

Tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana a gaban babbar kotun Southwark da ke birnin Landan a ƙasar Birtaniya domin zaman farko na shari’ar da ake yi mata kan zargin cin hanci da rashawa.

Diezani wadda ta rike mukamin ministar man fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015 ita ce mace ta farko da ta taba rike wannan mukami a Nijeriya, sannan ita ce mace ta farko da ta zama shugabar ƙungiyar ƙasashen da ke fitar da man fetur ta duniya wato OPEC.

An sanya shari’ar cikin jerin shari’o’in kotu a daki na takwas a gaban Mai shari’a Thornton, inda kotun ta fara sauraron shari’ar ne da nufin shirya cikakken zaman shari’a da aka tsara farawa a ranar 26 ga watan Janairu na shekarar 2026.

Kotun ta fara gudanar da matakan farko da suka haɗa da batutuwan fasaha da kuma tantancewa, inda Diezani ta halarci zaman kotun a makon nan domin wadannan matakai na farko kafin fara cikakken shari’a.

Diezani mai shekaru 65 tana kan beli tun lokacin da aka kama ta a birnin Landan a watan Oktoban shekarar 2015, kuma ta musanta dukkan tuhume-tuhume guda shida da ake yi mata a gaban kotu.

Hukumar yaki da manyan laifuka ta ƙasar Birtaniya ta gurfanar da ita a hukumance a shekarar 2023, bisa zargin karɓar cin hanci a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015, tana mai zargin cewa ta yi amfani da ikon da take da shi a Nijeriya wajen karɓar fa’idodin kuɗi domin ba da kwangiloli masu darajar fam miliyoyi.

Takardun tuhuma sun nuna cewa Diezani ta amfana da akalla fam Dubu Ɗari ta hanyar tsabar kuɗi, motocin haya tare da direba, tafiye-tafiye da jiragen sama masu zaman kansu, da kuma amfani da gidaje da dama a birnin Landan, baya ga kayan daki, gyaran gidaje, biyan kuɗin makarantu masu zaman kansu, da kyaututtuka daga manyan shagunan kayan alatu.

An bayyana cewa cikakken shari’ar zai fara ne a ranar Litinin 26 ga watan Janairu, kuma ana sa ran shari’ar za ta ɗauki tsawon makonni goma zuwa goma sha biyu, yayin da wasu mutane biyu ma suke fuskantar shari’a a wannan batu na cin hanci da rashawa tare da ita.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here