Tsohon Gwamnan Mulkin Soja na Jihar Kaduna, Col. Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya bukaci Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, da ya dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, bisa zargin lalata da wata ‘yar yawon buɗe ido ’yar kasashen waje.
Umar ya yi wannan kira ne a cikin wata budaddiyar wasika mai kwanan wata 22 ga Nuwamba, 2026, wadda ya aikawa Gwamna Radda, bayan yaduwar wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ake zargin ya nuna basaraken na aikata abin da bai dace ba ga wata farar fata mai yawon bude ido.
A cikin wasikar, tsohon gwamnan sojan ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, yana mai cewa idan aka tabbatar da zargin, hakan zai zama cin zarafin mutunci da nauyin da ke tattare da sarautar gargajiya.
Ya ce matsayin Sarkin Daura na kunshe da manyan nauyin da suka shafi tarbiyya, al’adu da tarihi, don haka duk wanda ke rike da irin wannan babban mukami ya kamata ya kasance mai nuna mutunci, kamun kai da kyakkyawan hali.
Umar ya bayyana damuwarsa kan cewa zargin na iya kara rage amincewar jama’a ga ɓangarorin sarauta, musamman ganin yadda ya ce a baya ma an samu rahotannin zargin amfani da karfin iko da Sarkin ya yi.
“Lamarin baya-bayan nan, ya sanya batun ya kai wani mataki na daban mai tsanani, kuma yana bukatar daukar matakin gaggawa,” in ji shi.
Saboda haka, ya yi kira ga Gwamna Radda da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki da dokoki suka ba shi wajen dakatar da Sarkin nan take, har sai an gudanar da cikakken bincike mai zaman kan shi, adalci da gaskiya kan zargin.
Read also: Juyin Mulki: Dalilin Da Yasa Muka Karbe Mulki Daga Hannun Shugaba Ali Bongo – Sojojin Gabon
Umar ya jaddada cewa dakatarwar da ake bukata ba za a dauke ta a matsayin tabbatar da cewa Sarkin ya aikata laifi ba, sai dai matakin da ya dace domin tabbatar da bin diddigin lamarin da kuma kare martabar masarautar Daura yayin da ake gudanar da bincike.
Ya kuma yi kira da a cire Sarkin daga sarautar ba tare da bata lokaci ba idan har aka tabbatar da zargin.
A cewarsa, babu wani mutum da ya kamata a dauke shi a matsayin wanda ya fi karfin hukuntawa, ko da kuwa shekarunsa, matsayinsa ko ikon sarautar gargajiyarsa.
Tsohon gwamnan ya kuma yi gargadin cewa barin lamarin ya dade ba tare da an dauki mataki ba, na iya jefa nɓangaren sarauta cikin kunya a idon jama’a tare da raunana martabarsu.
“Masarautun gargajiya na ci gaba da kasancewa muhimman ginshikan al’ummarmu. Kiyaye su da kuma ci gaba da kasancewarsu masu tasiri ya dogara sosai da halaye, gaskiya da dabi’un wadanda aka damka musu shugabancinsu,” in ji shi.
Read also: Trade | Nettruyen – Khám Phá Thế Giới Truyện Tranh Đa Dạng và Hấp Dẫn | 1-2025
Umar ya bukaci Gwamnan Katsina da ya dauki mataki cikin gaggawa, yana mai cewa bai kamata halayen mutanen da aka damka wa shugabancin gargajiya su zama sanadin lalata martabar hukumomin da suka dade daruruwan shekaru suna wanzuwa ba.













































