Wani matashi da ake zargin mai kwacen wayar Salula ne, sun kashe wani babban hafsan sojan ruwa, Commodore M. Buba, wanda ke yin kwas a kwalejin rundunar soji da ke Jaji, a ranar Asabar, 7 ga watan Yuni, a kusa da gadar sama ta Kawo da ke Kaduna a lokacin da yake kokarin gyara tayar motarsa.
Majiyar sojojin ta bayyana cewa jami’in, wanda babban dalibin kwas ne a AFCSC Jaji, ya tsaya a wata tashar mota da ke kusa da gadar a kan hanyarsa ta komawa Jaji, domin sauya tayar motar da ta samu matsala a lokacin da lamarin ya faru.
A cewar shaidun gani da ido, sun bayyana cewa, wani matashi ne ya nemi jami’in da ya ba shi wayarsa ta hannu, amma bayan da ya yi turjiya ne sai ya caka masa wuka a kirji.
An garzaya da jami’in wani asibiti da ke kusa, amma an tabbatar da cewa ya mutu bayan isa asibitin da shi.
Tuni dai aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na Asibitin Sojojin Najeriya na 44 da ke Kaduna.
A wani ci gaba kuma, wani dan kungiyar sintiri ta Vigilante mai suna Suleiman Dahiru, wanda ya yi yunkurin shiga tsakani yayin rikicin, shi ma maharin ya caka masa wuka a hannu.
Sai dai jama’ar da suka taru a wurin sun yi nasarar hallaka mai kwacen wayar.
A nasa bangaren, mai magana da yawun Rundunar Soji da kuma Kwalejin sojin, Laftanal Kanal Umar Adamu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayanin mutuwar jami’in.












































