Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin jama’a, Aliyu Audu, ya mika takardar murabus dinsa a yau Litinin.
A wata wasika mai shafi daya mai dauke da kwanan wata 8 ga watan Yuni kuma ta hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Audu ya rubuta cewa, “Na rubuta ne domin in mika takardar murabus dina nan take.
Na gode wa shugaban kasa bisa damar da ya ba ni na yi wa kasa ta hidima karkashin jagorancin ku mai hangen nesa.”

Aliyu Audu
Ya kuma yaba wa tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale, wanda shawarar da ta sa aka nada shi a ranar 26 ga watan Agusta, 2023.
An nada Audu mukamin ne a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2023, kuma shugaba Tinubu ya amince da nadin nasa a hukumance a ranar 9 ga Oktoba, 2023.
Wasikar ta ci gaba da cewa, “Abun alfahari ne na ba da gudummawa ga kokarin sadarwar jama’a na wannan gwamnati.”
Sai dai har yanzu fadar shugaban kasa ba ta mayar da martani kan murabus din Audu ba har zuwa fitar da wannan rahoto.












































