Alhaji Murtala Sule Garo, mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, ya yi kira ga tsoffin gwamnonin Kano da sauran shugabannin siyasa da su ajiye banbance-banbancen su domin ci gaban jihar.
Yayin wani taron cin abincin dare da bada lambar yabo da ƙungiyar tsoffin ‘yan majalisar dokoki ta Kano ta shirya, Garo ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin shugabanni wajen inganta cigaban jihar.
Garo ya nuna damuwa kan yadda tsoffin gwamnonin wasu jihohi, kamar Zamfara, ke haɗuwa don ci gaban jiharsu, yayin da hakan ke da wahala a Kano.
Ya roƙi shugabannin su yi aiki tare ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba domin kawo cigaba da cigaba ga Kano.
Ya kuma yabawa tsoffin ‘yan majalisar bisa haɗin kansu, yana mai cewa idan wannan haɗin kai ya dore, jihar Kano za ta samu ci gaba sosai.
Wannan kira ya zo ne a lokacin da ake bukatar haɗin kan shugabanni don magance kalubalen cigaban jihar.