Gwamnan Kwara ya cire wa dalibai da talakawa kudin mota tare da ba su tallafin kudi

330026241 758940668896166 723878447724009037 n
330026241 758940668896166 723878447724009037 n

Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince a rika daukan dalibai da ‘yan fansho da sauran jama’a talakawa masu rauni kyauta a motocin haya na bas domin rage musu radadin wahalan karancin mai da na naira.

Haka kuma gwamnan ya amince a rika bai wa matan da mazajensu suka rasu da ‘yan fansho da masu motocin sufuri da ‘yan kasuwa da kananan manoma da sauran talakawa a jihar taimakon kudi, inda za a rika tura musu kudin.

Ya ce hukumar shirin bunkasa rayuwar jama’a ta jihar ce (Kwara State Social Investment Programme wato KWASSIP ), za ta aiwatar da shirin tainmakon.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya fitar a jiya Alhamis, ya ce gwamnan ya umarci KWASSIP ta gaggauta tsara yadda za a gudanar da shirin domin saulkaka wa jama’a halin da suke ciki.

A sanarwar, ya ce, gwamnan ya kuma bayar da umarnin sanya motocin bas-bas na kyauta a wasu hanyoyi da dalibai da malaman manyan makarantu suka fi bi a babban birnin jihar, inda aka fi shan wuyar rashin man.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here