Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin APC kan zanga-zanga

Tinubu, APC, Da Dumi-Dumi, Shugaba, shiga, ganawa, gwamnonin, zanga-zanga, najeriya
Yanzu-yanzu shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya shiga ganawa da Gwamnonin jam’iyyar APC, karkashin kungiyar gwamnonin (Progressives Forum) a fadar...

Yanzu-yanzu shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya shiga ganawa da Gwamnonin jam’iyyar APC, karkashin kungiyar gwamnonin (Progressives Forum) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara da misalin karfe 1:00 na dare ya biyo bayan kiraye-kirayen da ake yi na zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki a fadin kasar.

Ko da yake ba a san ajanda na taron na ranar Alhamis ba, ana iya danganta shi da zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar 1 da 10 ga watan Agusta 2024.

Karin labari: Hukumar NDLEA ta cafke mutum 22 masu safarar kwayoyi a Kano

Zanga-zangar, wacce aka shirya a karkashin taken ‘EndBadGovernance,’ ta samu karbuwa sosai a shafukan sada zumunta duk da cewa wadanda suka shirya zanga-zangar ba a bayyana sunansu ba, ba tare da wata kungiya da ta dauki alhakinta a hukumance ba.

Wannan taron ya biyo bayan kammala taron kungiyar gwamnonin Najeriya da aka yi a daren Larabar da ta gabata, kuma ya biyo bayan soke taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa da aka shirya gudanarwa a yammacin ranar Alhamis.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da ministocin kudi da kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki, Wale Edun da Abubakar Bagudu..

Karin bayani na tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here