Kimanin mutane tara ne suka rasa rayukansu, wasu 11 kuma suka jikkata a wani hatsarin mota damm da ya afku a hanyar Malumfashi zuwa Kafur a jihar Katsina.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Aliyu Ma’aji, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa hadarin shi kadai ya shafi wata motar safa mai dauke da mutane 20.
Ma’aji ya danganta faruwar hatsarin da gudu ne sakamakon yadda direban motar ya rasa sarrafa motar.
Karin karatu : Sallah: Hukumar kiyaye hadɗura FRSC za ta baza jami’ai 1,889 a Kano
Don haka ya bukaci masu ababen hawa da su guji yin gudu da wuce gona da iri da kuma tukin ganganci a lokacin bukukuwan sallah.
Hakan a cewarsa, ya janyo asarar rayuka duk da kokarin da gwamnati ke yi na gina hanyoyi masu kyau. (NAN










































