Tinubu ya taya El-Rufai murnar cika shekaru 65, ya yaba da gudunmawar da ya baiwa dimokuradiyya

Bola Tinubu and Nasir El Rufai

Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai murnar cika shekaru 65 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin “Mai mulki, malami, kuma dan siyasa” wanda aka fi sani da “hanzari da hazaka.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Tinubu ya amince da rawar da El-Rufai ya taka a matsayin wanda ya kafa jam’iyyar APC da kuma gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zabuka uku a jere.

Sanarwar ta samu sa hannun Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin ayanai da Dabaru a ranar 16 ga Fabrairun 2025.

Karanta: Tinubu ya sauka a Ethiopia don halartar taron AU

Tinubu ya kuma yabawa “kokarin da tsohon ministan ya yi na tabbatar da dimokradiyya; kyakkyawar hidimarsa ga al’umma, da kuma nasiha ga matasa masu tasowa.”

El-Rufai wanda ya rike mukamin Darakta-Janar na Ofishin Kamfanonin Gwamnati kuma Ministan Babban Birnin Tarayya daga 2003 zuwa 2007, ya yi Gwamnan Jihar Kaduna na tsawon shekaru takwas.

Shugaban ya yi masa fatan “samun koshin lafiya da karfi don ci gaba da yi wa kasa hidima.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here