Jihar Ribas: Kotu ta musanta bada belin magoya bayan Fubara

Kotu, musanta, magoya baya, jihar ribas
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ranar Litinin ta yi watsi da bukatar belin da magoya bayan gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara suka shigar...

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ranar Litinin ta yi watsi da bukatar belin da magoya bayan gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara suka shigar, dangane da fashewar majalisar dokokin jihar.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Chime Eguma Ezebalike da Prince Lukman Oladele da Kenneth Goodluck Kpasa da kuma Osiga Donald tare da Ochueja Thanksgod.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da su gaban kuliya da laifin ta’addanci ne biyo bayan zarginsu da tada bam a majalisar dokokin jihar Ribas a watan Oktoban 2023, tare da zargin su da kashe wasu ‘yan sanda.

Karanta wannan: Masu zanga-zanga sun rufe hanyoyi a Minna

A ranar 30 ga Oktoba, 2023, wani fashewa ya afku a harabar majalisar dokokin jihar, lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin wasu ‘yan majalisar dokokin kasar nan na yunkurin tsige Fubara.

An bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan kunar bakin wake ne suka jefa bam a harabar ginin da misalin karfe 9:25 na dare, lamarin da ya haddasa gobara a ginin.

Sai dai wadanda ake tuhuma na daya zuwa na uku sun nemi belinsu bisa la’akari da yanayin kiwon lafiya.

Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin a Abuja Mai shari’a Bolaji Olajuwon ya ki amincewa da bukatar.

Karanta wannan: Masu kiwon kaji sun koka da asarar Naira Tiriliyan 3 kan tabarbarewar Tattalin Arziki

Ta ce ana tuhumar wadanda ake tuhumar ne da laifin kisa, wanda ya shafi ta’addanci da kuma kisan kai.

Olajuwon ya kara da cewa babu wata shaida da ke nuna cewa cibiyoyin da ke gidan gyaran hali ba za su iya biyan bukatun lafiyar wadanda ake kara ba.

Ta kara da cewa, shaidun da ke gaban kotun sun nuna cewa kwararru a cibiyar kiwon lafiya suna da kwarewa da kuma isassun kayan aiki don kula da yanayin wadanda ake tuhuma.

Daga baya an dage sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Febrairun shekarar nan don sauraren karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here