Da Dumi-Dumi: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar Rarara a Katsina

Rarara, mahaifiyar, 'yan bindiga, sace, Katsina Jami'an, tsaron, DSS, kama, fansar, kudin, makarfi
Jami’an tsaron farin kaya na DSS, sun kama mutum daya cikin wadanda ake zargin sune suka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara tare da kwato Naira miliyan 26...

A daren ranar Juma’a ne aka sace Hajiya Halima Adamu, mahaifiya ga shahararren mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu Rarara.

An sace ta ne a gidanta da ke kauyen Kahutu a karamar hukumar ‘Danja a jihar ta Katsina da misalin karfe 1:00am na tsakar dare kamar yadda wata majiya a kauyen Kahutu ta tabbatar.

Karin labari: Rundunar Sojin Najeriya ta karawa jami’arta girma

A cewar majiyar, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne cikin dare inda suka yi awon gaba da mahaifiyar tasa.

Saidai a labarin da ya fito daga jaridar DCL Hausa ta rawaito cewa Rarara ya tabbatar da faruwar lamarin tare da neman rokon al’umma da su taimake su da addu’o’in samun dauki ga Allah (S.W.T) domin bayyanar mahaifiyarsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here