Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a. Ya ce , hukumomin biyun suna yi wa wadanda ake zargin tambayoyi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Yau Juma’a 28 ga watan Yuni 2024 da misalin karfe 0130 ne aka samu labari a hedikwatar ‘yan sanda ta Danja cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka mamaye gidan wata mai suna Hauwa’u Adamu mai shekaru 75 da haihuwa. kauyen Kahutu, karamar hukumar Danja, jihar Katsina kuma sun yi garkuwa da ita.
“Bayan samun rahoton ba tare da bata lokaci ba DPO Danja ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da nufin kamo masu laifin tare da kubutar da wanda abin ya shafa.
Yan sanda na cika gaba da binciken lamarin.
Idan dai za a iya tunawa Rarara shi ne shugaban mawakan shugaban kasa a zamanin tsohuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma wakokinsa sun taka rawar gani wajen zaburar da magoya bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu musamman a tsakanin al’ummar Hausawa a Najeriya.