Matatar Mai ta Dangote ta rage farashin fetur da dizal

IMG 20240829 WA0005

Matatar mai ta Dangote ta rage farashin sayar da man fetur, da kuma dizal, lamarin da ya zama karo na farko na rage farashi bayan karin farashi da aka samu a kwanakin baya.

Bisa sabon jadawalin farashin da matatar ta fitar ranar 10 ga watan Maris 2026, farashin fetur daga ma’ajiyar matatar ya ragu da Naira 100 inda ya sauka zuwa Naira 1,075 kan kowace lita, daga Naira 1,175 da yake a baya.

Matatar ta kuma bayyana cewa fetur da ake kaiwa ta hanyar jigilar ruwa daga bakin teku yanzu za a sayar da shi kan Naira 1,050 kan kowace lita, wanda ke nuna dan bambancin farashi ga kayayyakin da ake kaiwa ta ruwa.

Haka kuma, farashin lodin dizal, ya ragu zuwa Naira 1,430 kan kowace lita, wanda ke nuna raguwar Naira 190 daga farashin baya na Naira 1,620 kan kowace lita.

Kamfanin ya bayyana cewa farashin lodin da aka ambata ba ya hada da kudaden haraji da hukuma mai kula da harkokin man fetur ta kasa ke karba.

Raguwar farashin ta zo ne a daidai lokacin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fara sauka, lamarin da ya rage matsin farashi a kasuwar man fetur ta duniya tare da yin tasiri ga farashin kayayyakin a bangaren sayarwa.

Masu nazarin harkokin masana’antar mai sun bayyana cewa raguwar farashin na iya kawo saukin dan lokaci ga ‘yan kasuwa da masu sayen mai da yawa, wadanda suka fuskanci tashin farashin lodin mai cikin sauri a kwanakin baya.

Masu ruwa da tsaki a kasuwar man fetur yanzu suna sa ido domin ganin yadda sabon farashin daga ma’ajiyar matatar zai ratsa ta wuraren ajiya daban-daban tare da sauya farashin sayar da fetur a gidajen mai a fadin kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here