Fassarar Aminu Bala Madobi-Daga Kano
Jam’iyyar APC Me Mulkin Kasa ta nada Malam Yusuf Bala Ibrahim a matsayin Daraktan yada labarai na jam’iyyar a matakin kasa.
A cikin wata wasika da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce nadin Bala Ibrahim a matsayin daraktan Hulda da Jama’a na Jam’iyar ya fara aiki ne daga ranar 1 ga Satumba, 2022.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Bala Ibrahim, gogaggen dan jarida, babban marubuci kuma Mai sharhi edita ne a Matakin Nahiyar Afirka dakuma al’amura na Gabas ta Tsakiya.
Bala Ibrahim, dan asalin jihar Kano, ya kasance mai baiwa tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris shawara kan harkokin yada labarai, daga 2016 zuwa 2019 kuma mai ba da shawara, ayyuka na musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
”Yayin da muke taya ka murna kan nadin da akayi maka, muna fatan za ka bada taka gudun-mawar ta hanyar gudanar da ayyukanka cikin nasara da kwanciyar hankali” Inji sanarwar.














































I like your paper and I wants to be one of your friend.
Thanks alot Garba Muazu we really appreciates