Gwamnatin Birtaniya ta yi alƙawarin ware Fam 117 miliyan (dalar Amurka miliyan 150) a cikin shekaru 4 domin inganta tsaron al’umma musulmai a ƙasar.
Gwamnatin ta ce za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗin domin ƙara matakan tsaro a masallatai da makarantun koyar da addini da wuraren da musulmai ke taruwa.
Haka kuma ta ba da tabbacin cewa ba za a lamunci yi wa musulmin ƙasar barazana ko kalaman ƙiyayya ba.
Karin labari: Isra’ila na ci gaba da ruwan wuta a Gaza duk da shigowar Ramadan
Sanarwar na zuwa ne bayan alƙawarin da gwamnatin ta ɗauka na kashe dala miliyan 90 don bayar da kariya ga Yahudawa.
Tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas ake samun ƙaruwar ƙiyayya tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma yahudawa mazauna Birtaniyar.