Daga Halima Lukman
Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun saki Daniel Ojukwu, dan jaridan da ke aiki da Foundation for Investigative Journalism (FIJ).
Sakin sa dai ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyin fararen hula suka yi a Abuja babban birnin tarayya.
Ojukwu, wanda ya bace da lambobin wayarsa a kashe, kuma abokan aikinsa ba a san inda yake ba, sai da aka gano cewa ‘yan sanda sun tsare shi, ya sake samun ‘yancinsa a ranar Juma’a.
Daniel Ojukwu, dan jaridar FIJ da wasu jami’an rundunar ‘yan sandan farin kaya (IRT) na babban sufeton ‘yan sanda suka yi garkuwa da shi, ya samu ‘yanci bayan kwanaki 10 a hannun ‘yan sanda,” FIJ ta rubuta a shafinta na yanar gizo game da sakin Ojukwu.
Ojukwu ya bace ne a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, lambobinsa a kashe, kuma abokan aikinsa, ‘yan uwa da abokan arziki ba a san inda yake ba.
Da ga karshe Daniel Ojukwu ya fito, ya Kuma godewa ‘yan Najeriya.