Hukumar tara haraji ta ƙasa ta bayyana cewa wata gobara ta tashi a ɗaya daga cikin ofisoshinta da ke hedikwata a Abuja a ranar Asabar, lamarin da ya jawo lalacewar wasu sassan ginin.
Sikiru Akinola, mataimaki na musamman kan harkokin fasaha da wallafe-wallafe ga shugaban Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa FIRS, Dakta Zacch Adedeji, ya bayyana cewa wutar ta tashi ne a bene na huɗu na ginin, inda jami’an tsaro da ke bakin aiki suka ɗauki matakin gaggawa tun da wuri domin hana bazuwarta zuwa sauran sassan ofishin.
Tare da taimakon hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja da sauran hukumomin bayar da agajin gaggawa, an samu nasarar shawo kan gobarar cikin lokaci, tare da hana ta yaɗuwa zuwa wasu gine-gine ko ofisoshi.
Hukumar ta tabbatar da cewa babu asarar rayuka a sakamakon gobarar, sai dai wasu ofisoshi da ke cikin benon da abin ya shafa sun samu lalacewa mai yawa.
An kuma fara bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, inda rahotannin farko ke nuni da yiyuwar matsalar wutar lantarki a matsayin sanadi.
A halin yanzu, hukumar ta fara nazari da ƙarfafa dukkan matakan tsaro na cikin gida domin rage yiwuwar faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
NAN













































