Kano ta sake fasalin hukumar Zakka da Hubsi, ta kafa kwamitin tantance kungiyoyin Musulunci na kasashen waje

Kano Map
Kano Map

Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sake fasalin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar Kano, inda ta bayyana Dokta Ibrahim Mu’azzam Maibushira a matsayin shugaban zartarwa.

Kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a karshen taron majalisar da aka gudanar a dakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin Kano.

A cewar sanarwar mambobin sun hada da, Dr. AbdulMutallab Ahmed a matsayin kwamishina na daya, Dr. Lawi Sheikh Atiq kwamishina na biyu na hukumar.

“Garba ya kuma lissafa sunayen mambobin hukumar da suka hada da Sheikh AbdulWahab Abdallah, Alhaji Aminu Dantata, Alhaji Aliko Dangote da kuma Alhaji AbdulSamad Rabi’u,” in ji sanarwar.

“Sauran mambobin, in ji shi, sun hada da wakilan masarautu guda biyar a jihar, wakilan ma’aikatar yada labarai, ma’aikatar harkokin addini, wakilan kasuwannin Kurmi, Rimi Kwari da kuma Singer”

‘’ Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kafa kwamitin tantance kungiyoyin addinin musulunci na kasashen ketare, wanda Farfesa Sani Zaharaddeen, babban limamin Kano zai kasance a matsayin shugaba; Dr. Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini, mataimakin shugaba da Auwalu Shehu Yakasai a matsayin sakatare.’’

“Ya ce ofishin sakataren gwamnatin jiha ne zai samar da wakilan majalisar masarautu da hukumomin tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here