Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwalejin horar da ma’aikatan gidan gyaran hali

Nigeria Prisons Service NPS
Nigeria Prisons Service NPS

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwalejin horas da ma’aikatan gidan gyaran hali ta Najeriya da ke jihar Kebbi tare da kaddamar da rukunin farko na jami’ai 100 da za a horas da su kan yadda ake tafiyar da fursunoni na yau da kullun domin kawo kawo gyara kan yadda ake gudanar da aikin.

Kwamandan kwalejin Hamisu Isa wanda ya bayyana haka a lokacin da aka fara bayar da horon a garin Makera da ke wajen babban birnin jihar, Birnin Kebbi, ya ce mahalartan sun fito ne daga kwamandojin hukumar da dama kuma za su dauki horon na tsawon watanni uku a kwalejin.

Isa ya ce baya ga horon kan yadda ake tafiyar da fursunonin, horon wanda ya kasance na wadanda suke mukamin mataimakin Sufeto na gidan yari (DSPs) zai baiwa jami’an damar samun kwarewa kan jagoranci.

A nasa bangaren, gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na taimakawa hidimar a inda ya dace.

Bagudu ya ce gwamnatinsa ta nuna jajircewa ta hanyar bayar da tallafin makarantar sakandare a maimakon wani fili da hukumar ta bukata domin kafa kwalejin horarwa.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, ya bayyana kawo kwalejin zuwa kauyen Makera, jihar Kebbi daga cikin jahohi bakwai na Arewa maso Yamma a matsayin wani abu da zai kawo wa jihar Ci gaba.

Ya kuma bukaci mahalarta taron da suka fito daga jihohi 36 na Najeriya da FCT, da su samu nutsuwa a Kebbi, su samu sabon ilimin, horon da za a yi na tsawon watanni uku, tare da yin tasiri mai kyau ga fursunonin da ake tsare da su na Jihohi daban-daban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here