Babu dokar da ta ce sai na gama NYSC za a naɗa ni minista – Hannatu Musa Musawa

No Law Bars Me From Being Minister While Serving As Corps Member Says Hannatu
No Law Bars Me From Being Minister While Serving As Corps Member Says Hannatu

Ministar Al’adu ta Najeriya Hannatu Musa Musawa ta musanta zargin da ake yi mata na karya dokar ƙasar bayan naɗa ta a muƙamin duk da cewa ba ta kammala hidimar ƙasa ta NYSC ba.

A Cikin wani martani da ta fitar a ranar Lahadin nan, ministar wadda ‘yar asalin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ce, ta ce “babu wata doka da na karya”.

“Dole ne na fito na faɗa cewa babu wata doka a Najeriya da ta ce shugaban ƙasa ko wata hukuma ba za su iya naɗa mutumin da yake hidimar ƙasa a muƙami na siyasa ba,” in ji ta.

Kafar sadarwar BBC Hausa ta ce, sai dai, Kakakin hukumar hidimta wa kasa, National Youth Service Commission (NYSC), Eddy Megwa, ya faɗa wa Daily Trust cewa “ta karya doka kuma muna duba yiwuwar ɗaukar matakin da ya dace” a kanta.

A ranar 21 ga watan Agustan ne Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Hannatu – wadda yanzu haka take gudanar da hidimar ƙasar a Abuja – a matsayin minista tare da sauran mutum 45.

Hannatu ta tabbatar da cewa tun a 2001 aka tura ta hidimar ƙasar zuwa jihar Akwa Ibom amma ta ɗage aiwatarwa sai a 2023 ta ci gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here