Gwamnatin tarayya ta shawarci gwamnatocin jihohin kasar nan da su kasance cikin shiri domin yakar ambaliyar ruwa biyo bayan karuwar magudanar ruwa a kogin Benue.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Farfesa Joseph Utsev da karamin ministan ruwa da tsaftar muhalli Bello Muhammad Goronyo ne suka bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Asabar.
“Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya ta lura da karuwar yawan magudanar ruwa a cikin tsarin kogin Benue, inda aka yi rijistar yawan kwararar ruwa na 8.97m zuwa yau.”













































