Cin zarafin Naira na nan a matsayin laifi mai ɗauke da hukunci – CBN

cbn new

Babban Bankin Najeriya CBN ta ja hankalin ‘yan ƙasa da su daina cin zarafin kuɗin Naira domin kuwa alamar ƙasa ce da ta cancanci girmamawa da kyakkyawan mu’amala.

A wurin taron Babban Bankin Najeriya da aka gudanar a Enugu a ranar talata, mukaddashiyar daraktar sashen yaɗa labarai, Hakama Sidi Ali, ta bukaci jama’a su kula da tsabtar kuɗi tare da tabbatar da cewa duk wani cin zarafi na Naira har yanzu laifi ne da ake hukunta wanda aka kama.

Ta bayyana cewa jama’a su guji yayyafa kuɗi, sayar da kuɗi, lalatawa ko ƙirƙira kuɗin bogi domin kuwa Naira muhimmin abu ne da ke nuna alamar ƙasa, tare da nanata cewa kulawa da kuɗi na daga cikin hanyoyin inganta al’adun kuɗi da kuma ƙarfafa tsarin biyan kuɗaɗe.

Sidi Ali ta shawarci al’umma da su dogara kacokan ga bayanai na gaskiya daga tashoshin Babban Bankin Najeriya kawai domin kaucewa yaɗuwar bayanan ƙarya, musamman a kan manufofin kuɗi da dokoki.

Ta kuma bayyana cewa gyare-gyaren Bankin kamar ɗaurewar manufofin kuɗi, daidaita farashin musayar kuɗi da ƙara bayyana bayanai sun taimaka wajen daidaita tsarin kuɗi da inganta hauhawar farashi da ajiyar ƙasa.

Ta ce shugabancin Bankin ƙarƙashin Olayemi Cardoso ya ɗauki matakan tabbatar da zaman lafiyar harkokin kuɗi, ciki har da ƙarfafa jarin bankuna, kaddamar da BVN na wadanda ba mazauna ƙasa ba da kuma ci gaba da gyare-gyare a tsarin biyan kuɗaɗe.

A wajen taron, mai kula da reshen Babban Bankin Najeriya na Enugu, Justice Agbeze, wanda Uche Ezike ya wakilta, ya kara jaddada muhimmancin kula da kuɗi, yana mai cewa manufar tsabtace takardun kuɗi na daga cikin muhimman manufofi na kare masu amfani da kuɗi da kuma ilmantar da jama’a.

Taron ya haɗa masana daga sassa daban-daban na Babban Bankin Najeriya domin wayar da kan mahalarta kan ci gaban tsarin biyan kuɗi, hakkin masu amfani da kuɗi, ayyukan microfinance da hanyoyin sarrafa takardun kuɗi.

Yayin taron jami’an sun bukaci jama’a su yi tambayoyi tare da shiga mu’amala domin tabbatar da haɗin kan jama’a wajen cimma ingantacciyar shigar kuɗi da bunƙasar tattalin arziki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here