Borno: Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda 31, Sun Damke 70 a Borno 

Army new new 678x349 1
Army new new 678x349 1

Hedkwatar tsaro ta kasa a ranar Alhamis, tace dakarun Operation Hadin Kai sun halaka kusan mayakan Boko Haram da na ta’addancin ISWAP 31 tare da kama wasu 70.

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, daraktan fannin yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ya sanar da hakan a Abuja yayin jawabi kan nasarorin da dakarun suka samu a makonni biyu da suka gabata.

Ya kara da cewa daga cikin 70 din da aka kama a yankin arewa maso gabas, 60 daga cikinsu duk ‘yan ta’adda suka samarwa kayan abinci, makamai da man fetur da sauransu. Sai dai rundunar sojin bata yi magana kan Gargash da Ngauri ba dake karamar hukumar Bama inda sojojin sama suka halaka wasu ‘yan ta’addan a maboyarsu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here