Jonathan Tunde Mark, wanda shine babbaan dan tsohon shugaban majalisar dattijai, sanata David Mark, ya mutu.
An tattaro rahotan cewa Tunde, mai shekaru 51, ya rasu a Kasar Birtaniya ranar Alhamis da daddare, bayan yasha fama da da cotar Kansa.
Mataimaki ga tsohon satanatan ya ta tabbatar da rasuwar ga jaridar Daily Independent da safiyar Juma’a.
Jama’a dai nata tururuwa wajan mika sakon ta’aziyar su zuwa ga David Mark.
An haife mirgayin 13 ga watan Oktuba na shekarar 1971 a garin Otukpo.













































