Kotu a birnin Maradi da ke Jamhuriyar Nijar ta yanke wa wasu matasa hukuncin ɗaurin shekara uku-uku a gidan yari, bayan samunsu da laifin naɗa da kuma yaɗa wani bidiyo da ke nuna wasu mata biyu suna madigo.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da mata 13 da namiji ɗaya.
Baya ga hukuncin ɗaurin, kotun ta ci tarar matan su 13 Sefa miliyan ɗaya kowace yayin da aka ci namijin tarar sefa miliyan uku kasancewarsa wanda ke da dandalin manhajar Whatsapp din da aka yadda wannan bidiyon.
BBC ta rawaitu makonni biyu da suka wuce ne dai aka fara gurfanar da mutanen 14 gaban kotun bisa zarginsu da aikata laifin yaɗa abu ta shafukan intanet da ka iya tayar da hankalin jama’a.
Laifin, a cewar lauya mai shigar da ƙara ya saɓawa dokar haramta aikata laifuka ta shafukan intanet.
Ya kuma nemi a yi mu su hukunci mafi tsanani na ɗaurin shekaru uku; wanda kuma shi ne kotun ta sanar a ranar Alhamis.
Jami’an tsaro na jandarma ne suka kakkama matasa bayan wani koke da wasu mutane suka yi kan yaɗa bidiyon na batsa.













































