Babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja, ta umarci shugaban kotun da’ar ma’aikata Danladi Umar, daya gabata a gaban zauren Majalisar dattijai domin bada rahoto kan cin zarafin da aka yiwa wani jami’in tsaro mai zaman kansa a Abuja.
Majalisar Dattawan ta bukaci Umar ya gurfana a gabanta bisa cin zarafin wani mai suna Clement Sagwak, dake bada tsaro a rukunin shagunan Banex Plaza dake Wuse, 2 a birnin Tarayya Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa tun da farko an yi zargin Danladi Umar, da cin zarafin Clement don ya umarce shi ya ajiye abin hawansa a inda ya kamata.
Da yake zartar da hukunci game da lamarin a ranar Alhamis, mai shari’a Inyang Ekwo, yace a matsayin Umar na Jami’in gwamnati dake gudanar da doka, ya cancanci ya gurfana a gaban Majalisar domin bada bahasi.
Mai shari’a Ekwo ya kuma yi watsi da rokon da Umar ya yi na neman a dakatar da bincikensa da majalisar dattawa ke shirin yi.











































