Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen matsalar tsaro – Isiak Amao

images 1
images 1

Babban Hafsan sojin saman Najeria Air marshal Isiaka Oladayo Amao yace ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

Hafsan sojin saman ya bayyana hakan a ranar juma’a yayin da ya ziyarci fadar gwamnatin Jihar Kano.

Yace kafin karshen wa’adin gwamnatin nan ya kare zasu tabbatar komai ya koma dai dai.

Shugaban hafsan sojin saman ya kuma godewa gwamnatin bisa ga tarba mai kyau da aka musu.

Da yake jawabi gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gode musu bisa ga zabar Kano domin gudanar da taron bikin cika shekaru 58 da kafuwar rundunar sojin sama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here