‘Yan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya ga hukumomi

BANDITS 1
BANDITS 1

Hedikwatar tsaron kasar nan ta ce ya zuwa ranar 16 ga watan Mayu mayakan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya ga hukumomi.

Daraktan yada labaran Hedikwatar, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a Abuja.

Ya ce mambobin kungiyar 1,627 sun mika wuya tare da iyalansu, da suka hadar da maza 331 da mata 441 da yara 855 sun mika wuya ga sojoji a yankuna daban-daban tsakanin 1 ga watan Mayu da kuma 14 ga watan.

Ya ce dakarun Najeriya na rundunar hadin kai sun kashe ‘yan ta’adda 43, tare da kama 20 da kuma ceto mutum 63 cikin wadanda aka kama a fadin arewa maso gabahsin kasar cikin mako uku.

Ya ce sun kashe kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa a Yuwe da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here