Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, ya yi watsi da rahoton ficewar sa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Namadi Sambo, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Umar Sani, ya fitar, ya bayyana rahoton sauya sheka a matsayin kage ne da nufin bata suna.
Sanarwar ta kara da cewa, hoton tsohon mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da ake yadawa a kafafen yada labarai, ya yi amfani da shi a labarin sauya shekar, tsohon hoto ne.
Sanarwar ta kara tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasan jigo ne kuma jagora a jam’iyyar PDP da ba shi da niyyar shiga wata jam’iyyar siyasa bayan wadda ya ke ciki.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Larabar da ta gabata ne aka samu labarin ficewar Sani Sidi, wanda ke zama na hannun daman tsohon mataimakin shugaban kasar zuwa jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna.
“An jawo hankalina bisa wani labari da ya yadu da ke cewa Mai Girma, Arc. Mohammed Namadi Sambo, GCON, tsohon Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya, ya koma jam’iyyar APC, wannan ikirari gaba daya karya ne.
NAN













































