Gwamnan Jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya ayyana hutu na kwanaki biyu a ranakun Alhamis da Juma’a domin bada dama don gudanar da zaɓen kananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.
Gwamnan tun da farko ya bai wa dukkan masu rike da mukaman siyasa mako guda su koma yankunansu domin yin kamfen da kuma tabbatar da nasarar jam’iyyar da ke mulki ta APC.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman, ya bayyana cewa Alhamis, 30 ga Oktoba, da Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025, za su kasance ranakun hutu a fadin jihar.
Ya ce wannan mataki yana da nufin bai wa masu jefa ƙuri’a damar zuwa rumfunan zaɓe domin kada ƙuri’unsu cikin walwala da lumana.
Usman ya bayyana cewa kasuwanni, bankuna, cibiyoyin kuɗi da ofisoshin gwamnati za su kasance a rufe a wadannan ranaku, yayin da zirga-zirga za ta kasance takaitacciya sai ga masu aikin dole kawai.
Ya ce gwamnati tana ƙarfafa al’umma da su fito da yawa domin gudanar da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya, tare da zaɓen shugabanni nagari da za su inganta ci gaban ƙananan hukumomi.
Sakataren ya ƙara da cewa gwamna Bago ya umarci hukumomin tsaro su tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, tare da tabbatar da tsaro a duk fadin jihar.










































