Jihar Abia ce ta fi Kano samun nasara a  sakamakon jarabawar NECO ta 2025 – Rahoto

Abba Kabir Yusuf sad 750x430

Jihar Abia ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarabawar kammala sakandare da hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) da ta fitar a bana, ba Kano ba, kamar yadda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi ikirari.

Gwamna Yusuf ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa Kano ce ta yi fice a jarabawar, inda ya danganta hakan da gyare-gyaren da gwamnatin sa ta aiwatar a fannin ilimi.

Sai dai binciken da aka yi ya nuna ba haka abin yake ba.

Rahoton ya tabbatar da cewa kaso mafi yawa na daliban Kano – fiye da rabinsu – sun kasa samun aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, wadanda ake bukata domin samun gurbin shiga jami’a.

Kano dai ta fi kowace jiha yawan ɗaliban da suka zauna jarabawar, amma wannan ba yana nufin ta yi nasara ba.

Kano ta zo ta 29 daga cikin jihohi 37 (ciki har da Babban Birnin Tarayya) wajen nasara, kuma ba ta kai ga zama sama da Lagos da Oyo kamar yadda gwamnan ya yi ikirari ba.

Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSCE ta 2025

Abia ce ta samu nasara mafi girma da kaso 83.31 cikin ɗari na daliban ta, yayin da Kano ta tsaya a kaso 49.84 cikin ɗari kacal.

Kididdigar NECO ta nuna cewa dalibai 1,358,339 suka rubuta jarabawar, daga ciki 60.26 cikin ɗari ne kawai suka samu aƙalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Jihar Abia ta yi fice da kashi 83.31 cikin ɗari, sannan Imo da Ebonyi suka biyo baya.

Jihohin da suka fi nasara guda goma sune: Abia, Imo, Ebonyi, Anambra, Bayelsa, Delta, Osun, Ogun, Lagos da Ekiti.

A gefe guda kuma, Kano na daga cikin jihohin da suka yi kasa a gwiwa tare da Yobe, Adamawa, Plateau, Borno, Jigawa, Katsina, Zamfara da Sokoto.

Rahoton ya kammala da cewa abin da gwamnan Kano ya jingina a matsayin “nasara ta farko” a zahiri yawan ɗaliban jihar ne kawai, ba nasarar sakamako ba.

Wannan ya nuna cewa fiye da rabin ɗaliban Kano sun kasa, duk da yawansu a cibiyoyin jarrabawar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here