Gwamnatin tarayya ta jaddada haramcin karɓar kuɗi a hannun ɗaliban makarantun fasaha

Tunji Alausa 750x430

Gwamnatin tarayya ta sake jaddada cewa duk kuɗin makaranta da waɗanda aka amince da su a Makarantun Fasaha na tarayya a fadin ƙasar nan kyauta ne, tare da gargaɗin daraktoci da masu gudanarwa da su guji kakaba wasu kuɗaɗe da ba su da tushe ga ɗalibai.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba ta hannun ma’aikatar a shafinta na X, inda ya ce gwamnati ce ke ɗaukar nauyin kuɗin makaranta domin tabbatar da daidaitaccen damar samun ilimin fasaha ga dukkan ’ya’yan Najeriya.

Ya ƙara da cewa babu wani jami’in makaranta da aka yarda ya tilasta iyaye ko masu kula da ɗalibai biyan wasu kuɗaɗen da ba su cikin tsarin, inda aka riga aka turawa makarantu duk takardun umarni don tabbatar da bin wannan doka.

Alausa ya bayyana cewa gwamnati na rufe kuɗaɗen da suka haɗa da masauki, kayan makaranta, littattafai, ƙa’idoji, kati na ɗalibi, kayan rubutu, ƙungiyoyi, hidimar lafiya, horon sana’o’i, lantarki da ruwa, tsaro, shafukan yanar gizo da sakamakon jarrabawa, ƙarin darussa da inshora.

Ya ce iyaye su rika kai rahoton duk wata bukatar neman kuɗi da ba ta dace ba kai tsaye ga ma’aikatar ta hanyar layukan waya ko imel da aka bayyana.

Sai dai ya fayyace cewa duk da cewar gwamnati ke ɗaukar nauyin kuɗin makaranta da muhimman abubuwa, ɗaliban da ke kwana a makaranta na buƙatar kawo wasu kayayyakin amfani na kansu kamar sabulu, zanen gado, barguna, da tufafi.

Haka kuma an ambaci wasu kayayyakin aiki na sana’o’i da za a buƙaci ɗaliban su bayar, ciki har da takardar A4 don rajista.

Ya bayyana wannan shirin a matsayin wani ɓangare na ajandar “Sabon Fatan” na shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ya ɗauki ilimin fasaha da koyar da sana’o’i a matsayin hanya ta gina ƙwarewar ɗan Adam da kuma ƙara wa ƙasar ƙarfi wajen yin gogayya a duniya.

Alausa ya jaddada cewa ba za a bari wani ɗan Najeriya ya rasa damar karatun fasaha saboda neman kuɗaɗen da ba su da tushe ba.

Ya ce an kafa tsarin sa ido don hukunta duk masu karya doka, tare da roƙon masu ruwa da tsaki da su taimaka wajen kare manufar kyauta ta ilimi domin makarantun fasaha na tarayya su samar da ƙwararrun matasa don cigaban ƙasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here